You are on page 1of 1

Amirka ta ce Duniya ta amince da Guaido

Gwamnatin Amirka ta bukaci duniya da ta amince da madugun adawar Venezuela a matsayin


shugaban kasar na hakika. Guaido dai ya ayyana kansa a matsayin shugaba.

Mataimakin shugaban kasar Amirka Mike Pence ne yace lokaci ya yi da Majalisar Dinkin
Duniya za ta amince da jagoran adawar kasar Venezuela Juan Guaido, a matsayin halattacen
shugaban kasa.

Mr Pence ya shaida wa kwamitin sulhu na majalisar ta duniya cewar fadar White House, za ta
mika daftarin bukatar kafa Guaido a matsayin shugaban na Venezuela, tare da nada wakilin
kasar a majalisar ta dinkin duniya.

Amirka dai na daga cikin kasashen duniya 50 da suka amince da Mr Guaido wanda tuni ya
ayyana kansa a matsayin shugaban kasa.

Ya kuma shawarci Mr Guaido, da ya hanzarta komawa birnin Carakas don isar da sako ga
Shugaba Nicolas Maduro.

Sai dai a bayyane take kasar Rasha na iya hawa kujerar na ki.

DW

You might also like