You are on page 1of 1

Sudan: Sojoji na tattaunawa da Al Bashir

Wasu bayyanai da har yanzu ba a tabbatar da gaskiyarsu ba na cewa sojoji na Sudan na can
na tattaunawa da Shugaba Umar Al Bashir domin ya yi marabus.

Kafar yada labari mallakar gwamnati ta Kasar Sudan ta sanar da cewar nan gaba kadan rundunar
sojojin kasar za ta bayyana wata sanarwa mai muhimmanci a game da halin rikicin siyasar da ake ciki
a kasar. Wannan sanarwa ta zo ne a daidai lokacin da dubban masu yin zanga-zanga suka yi dafifi a
gaban sansanin sojojin a birnin Khartum domin neman amanar sojojin da su kifar da
gwamnatin Umar Albashir daga mulki.

You might also like