You are on page 1of 1

An zabi kakaki biyu a majalisar dokokin

Bauchi
An samu rudani a ranar farko da aka bude sabuwar majalisar dokokin jihar Bauchi, inda
bangarorin da ke hamayya da juna suka zabi shugabanni daban-daban.

'Yan majalisa 11 na bangaren Gwamna Bala Mohammed na jam'iyyar PDP sun zabi Alhaji
Abubakar Y. Suleiman, wanda dan jam'iyyar hamayya ne ta APC. Sai dai ba shi jam'iyyar ke
so ba a matsayin kakakin majalisar.

Yayin da 20 da ke goyon bayan tsohon gwamna suka zabi Kawuwa Shehu Damina a
matsayin na su kakakin.

Ali Dan Iya yana cikin wadanda suka zabi Shehu Damina, kuma ya shaida wa manema
labarai cewa an shammace su ne tun farko a wajen zaben, hakan ya sa suka yi zama a wajen
harabar majalisar kuma suka zabi na su kakakin.

Sannan suka kuma zabi Tukur Ibrahim Toro a matsayin mataimakinsa.

"Doka ta ba mu damar yin zama a ko'ina in dai akwai sandar majalisa a wurin kuma akwai
sandar a farfajiyar majalisa.

"Umarnin jam'iyya muka bi muka zabe shi kuma dama mun zauna da shi mun ga irin
takunsa."

BBC ta yi kokarin jin ta bakin 'yan bangaren gwamna Bala Mohammed, inda aka tuntubi
shida daga cikinsu amma ba su amsa waya ba.

Mambobin jam'iyyar APC mai adawa guda 22 ne a majalisar, na PDP takwas, yayin da NNPP
ke da guda daya.

Shi dai Abubakar Y. Suleiman yana wakiltar Karamar Hukumar Ningi Ta Tsakiya ne, inda
Kawuwa Shehu Damina yake wakiltar mazabar Darazau.

Kasancewar jam'iyyar adawa ta APC ce ke da rinjaye a majalisar mai yiwuwa ne a ci gaba da


samun rikici game da ayyukan majlisar, da kuma musamman alaka tsakanin majalisa da
bangaren zartarwa a jihar.

You might also like